Ana taron kasa kan inganta sha'anin tsaro a Najeriya

Jami'an tsaro bakin aiki a Maiduguri
Image caption Jami'an tsaro bakin aiki a Maiduguri

An bude wani taron kolin na kwana biyu na kasa a Abuja babban birnin Najeriya a game da kalubalen da ya dabaibaye sha'anin tsaro a kasar.

Rundunar 'yan sandan kasar ce da hadin-gwiwar kamfanin jaridar Vanguard suka shirya taron wanda aka yi ma taken "magance kalubalen tsaro domin cigaban kasa".

Taron kolin dai ya zo ne kwana daya kacal bayan da wasu 'yan bindiga suka bude wuta kan gungun wasu mutane dake shirin Sallar Magariba a birnin Kano, inda suka kashe mutane ukku.

Karin bayani