An saki 'yan jaridar Almizan da aka kama

Nigeria
Image caption Kungiyar 'yan jarida ta kasa NUJ ta soki kamen na ma'aikatan Almizan

A Najeriya jami'an tsaro sun sako ma'aikatan jaridar Almizan biyu da suka cafke a jihar Kaduna.

'Yan jaridar Musa Mohammed Awwal da kuma Aliyu Saleh, an sako su ne bayan sun shafe sama da mako daya a hannun jami'an tsaron kasar.

"Duk da cewa an sako mu ba tare da wani sharadi ba, har yanzu wayoyinmu da sauran kayan aikinmu na hannun jami'an tsaron SSS," kamar yadda Musa Mohammed Awwal ya shaida wa wakilin BBC na Kaduna Nura Muhammad Ringim.

Ya kara da cewa sun ce har yanzu suna gudanar da bincike kuma da zarar sun kammala za su mika musu kayansu.

Kama 'yan jaridar na Almizan dai a ganin wasu 'yan jaridu ba zai rasa nasaba da wani labari da suka buga ba a bisa wasu matasa da rundunar hadin gwiwa ta ta cafke a garin Potiskum - jaridar kuma ta ce sun yi batan dabo.

Karin bayani