Ghana ta haramta shiga da tsaffin firij kasar

  • 1 Janairu 2013
Tsaffin na'urorin firij na kasuwa a kasar Ghana
Image caption Tsaffin na'urorin firij na kasuwa a kasar Ghana

Daga yau kasar Ghana ta haramta shiga da kwancen na'urar firji cikin kasar, don gurbatar yanayin da sinadaran dake cikin su ke haifarwa.

Tun a shekara ta 2008 majalisar dokokin kasar ta amince da sabuwar dokar da ta haramta shiga da kwancen firjin, wadda za ti fi aiki ne kan firjin da ake sayowa daga kasashen Tarayyar Turai.

Kasar ta Ghana ta ce daukar wannan mataki ya wajaba ne, saboda bukatar da ake da ita ta inganta makamashi da kuma kawo karshen illar da gas din da kwancen firjin ke fitarwa kan yi a kan muhalli.

Sai dai kuma, ba kowa ne ke farin ciki da wannan mataki ba, duk kuwa da cewa sun samu lokaci mai tsawo don shiryawa dokar.

Hukumar makamashi ta kasar Ghanan ta ce yanzu haka kusan gidaje miliyan biyu na da irin wadannan tsaffin firij-firij din; kuma mutanan da suka mika na su za su iya sayan sabbi akan farashi mai sauki.

Har yanzu kasashen Afurka da dama na shigar da tsaffin firij-firij dake da hadarin gaske.

Sai dai kuma shugaban hukumar makamashi ta Ghanan, Alfred Ofosu Ahenkorah ya ce yana fatan shirin da ake na kafa masana'antar kera firji zata samar da ayyuka.