An kashe mutane 60 a Ivory Coast

Image caption Lamarin ya faru ne a lokacin bukukuwan sabuwar shekara

Rahotanni sun ce akalla mutane 60 ne suka mutu a birnin Abidjan na kasar Ivory Coast sakamakon turmutsutsu a lokacin bukukuwan sabuwar shekara.

An kashe mutanen ne da daddare a tumutsetseniyar da ta kaure a lokacin da aker wasan wuta domin murnar shigawar sabuwar shekara, kamar yada gidan rediyon kasar ya bayyana.

Masu aikin ceto sun ce adadin wadanda suka mutu zai iya karuwa, kuma akwai yara kanana da dama da lamarin ya ritsa da su.

Shugaban kasar Alassane Quatarra ya ziyarci wadanda suka samu raunuka a sibiti, kamar yadda wani hoto da aka wallafa a shafinsa na Twitter, ya nuna shi tare da matarsa, a wani asibiti a birnin Abidjan.

Ya kuma ce gwamnati za ta dauki nauyin maganin da za a yiwa dukkan wadanda suka jikkata.

Shahararren mawakin Amurka Chris Brown

"Abin da ya faru a takaice tsakanin karfe biyu zuwa hudu na dare shi ne, mutane da dama na barin filin wasa domin tafiya gida daga wurin wasan da gwamnati ta shirya, daga nan ne matsalar ta fara. Mun samu tabbacin cewa mutane 200 sun samu munanan raunuka, " a cewar Frank Kodjo mai magana da yawun kungiyar agaji ta Red Cross a Ivory Coast.

Lamarin ya faru ne da sanyin safiyar ranar Talata a yankin Plateau na tsakiyar birnin.

Rahotanni sun kuma ce wasu daruruwan mutane sun samu raunuka.

Da dama daga cikin wadanda lamarin ya ritsa da su yara ne kanana.

Wadanda suka shaida lamarin sun ce an ga gawarwakin mutune da takalma da sauran kayayyaki warwatse a wajen filin wasan kwallon kafa na birnin inda lamarin ya afku.

Jami'an tsaro na wurin lokacin da jami'an gwamnati suka kai ziyara wurin. Kawo yanzu ba a san abinda ya haifar da lamarin ba.

"A yanzu rahotannin da muke samu na cewa mutane 263 ne suka samu raunuka. Kuma ya ritsa da mutane da dama, ciki harda kananan yara 'yan kasa da shekaru 15 da suka samu raunuka," kamar yadda Marius Kouassi, wani ma'aikacin jarida Abidjan Live news da ake wallafawa a intanet, ya shaida wa BBC.

Sai dai kawo yanzu babu tabbas kan yadda lamarin ya faru.

Sai dai wasu rahotanni sun ce dubban mutane na fita daga cikin filin wasan lokacin da wasu dandazon mutanen kuma ke kokarin isa tsakiyar birnin, abinda watakila ya sa jama'a suka firgita.

Filin wasan mai cin mutane 65,000 wanda aka sanya wa sunan tsohon shugaban kasar Felix Boigny, ya dauki bakuncin wani gagarumin wasa da shahararren mawakin nan dan Amurka Chris Brown ya gabatar a daren ranar Litinin.

Karin bayani