Jami'yyar PDP ta gaza a shekara ta 2012 - ACN

Goodluck Jonathan
Image caption Goodluck Jonathan ya yi alkawarin shawo kan matsalolin da kasar ke fuskanta

Jam'iyyun adawar Najeriya sun soki gwamnatin PDP mai mulki da cewa ba ta tabuka wani abin kirki ba a shekarar da ta shude, sai dai gwamnatin ta yi watsi da kalaman.

Babbar jam'iyyar adawa ta ACN ta yi zargin cewa yaudara ta fi yawa a cikin ayyukan gwamnatin shugaba Goodluck Jonathan.

Sai dai gwamnatin Najeriyar ta ce ta cimma nasarori masu yawa, kuma idan ba a yaba mata ba to bai kamata a kushe mata ba.

"Babu abin da gwamnatin PDP ta yi a shekara ta 2021 sai bata wa 'yan kasar lokaci da dukiya, saboda babu wani abin da gwamnatin za ta nuna na inganta rayuwar al'uma da ta yi," a cewar Senata Lawal Shu'aibu sakataren ACN na kasa.

Jiran gawon-shanu

Sai dai gwamnatin Najeriyar ta ce ba ta mamakin furucin da 'yan adawa ke yi, kamar yadda ministan yada labaran kasar Mr Labaran Maku ya shaida wa BBC.

"Aidama 'yan adawa ba za su taba yabonmu ba domin so suke su kwace iko daga hannunmu," a cewar Mr Maku.

Jam'iyyar ACN ta yi ishara da cewa idan gwamnatin Najeriya ba ta sauya salon takunta ta fuskar jagoranci ba to da wuya kasar ta ga wani abin alheri a wannan sabuwar shekarar.

Ta jaddada cewa idan irin tafiyar da gwamnatin shugaba Jonathan ta yi a baya ta isa abin misali, to yadda kasar ta cije a waje daya haka za ta ci gaba da kakarewa, ta dinga rabewa da za a yi za a yi, inda a karshe za ta bar 'yan kasar suna jiran gawon-shanu.

Jam'iyyar adawar ta shawarci gwamnati da ta yaki cin hanci bil hakki, idan dai tano so Najeriya ta bunkasa.

Sai dai Mr Labaran Maku ya bayyana cewa gwamnatin kasar ko a baya ma ba cijewa ta yi a wuru guda ba, shimfida ta yi ga ayyukan da za ta aiwatar nan gaba, wadanda ya ce 'yan kasar za su fara jin tasirinsu a cikin sabuwar shekarar.

Karin bayani