Pakistan ta saki karin 'yan Taliban 8

'Yan kungiyar Taliban na Afganistan
Image caption 'Yan kungiyar Taliban na Afganistan

Gwamnatin Pakistan ta ce ta saki karin wasu manyan 'yan kungiyar Taliban ta Afghanistan 8, don karfafa shirin sasantawar da ake yi a Afghanistan.

Mutane biyar ne kawai aka ambaci sunayen su, dukkan su kuma tsoffin Ministoci ne na gwamnati ko gwamnonin lardi.

To sai dai kuma babu sunan wani babban dan kungiyar ta Taliban cikin mutanen da aka saki watau Mullah Abdul Ghani Baradar, wanda mataimaki ne na shugaban Taliban Mullah Omar.

Mullah Abdul Ghani Baradar dai har yanzu na tsare a gidan Yari a Pakistan, duk kuwa da bukatar da gwamnatin Afghanistan ta gabatar ta neman a sake shi.

Gwamnatin Afghanistan ta yi marhabin da wannan yunkuri, amma tace tana son gano wadanda aka saki don tsoma su a shirin zaman lafiyar.