Sanatoci da Fadar White House sun cimma matsaya

Majalisar Dokokin Amurka
Image caption Majalisar Dokokin Amurka

Fadar White House ta Amurka da Sanatocin jam'iyyar Republican sun cimma matsaya kan batun kawar da kasar daga fadawa tsaka mai wuyar tattalin arziki.

Wannan kuwa ya kunshi karin haraji ga jama'a da rage kudaden da ake kashewa na gwamnati lamarin da ya yi barazanar jefa kasar cikin wani hali na gurguncewar tattalin arziki.

Ana dai kyautata zaton 'yan jam'iyar Democrat ma za su mara baya ga wannan matsaya da aka cimma.

Sai dai kuma babu wanda yace uffan kan batun cikin 'yan republican a majalisar wakilan kasar.

Jagoran 'yan republican a majalisar dattawa Mitch MacConnell ya ce an cimma matsaya da 'yan democrat kan dukkan batutuwan da suka shafi haraji a wannan sabuwar yarjejeniyar.

Ya kuma ce akawai bukatar kare Amurkawa da masu samar da ayyukan yi daga fuskantar karin haraji.

Mr MacConnell din ya Kuma yi kira ga majalisar dattawan da kada ta yi jan kafa game da batun.

Mai yiwuwa ne dai Sanatocin su kada kuri'a a kan sabuwar yarjejeniyar kafin wa'adi na tsakiyar dare agogon Amurkar.