An tsagaita wuta a Jamhuriyar Afrika ta tsakiya

car
Image caption 'Yan tawaye na kokarin korar shugaba Bozize

'Yan tawaye a Jamhuriyar Afrika ta tsakiya sun ce za su dakatar da amfani da karfin wajen neman hambarar da Gwamnatin Francois Bozize.

Saboda haka abinda suka sa a gaba a yanzu haka shi ne neman sasantawa da Gwamnati domin samun hanyoyin aiwatar da yarjejeniyoyin da suka sa hannu akai tare da Gwamnati.

Rundunar kiyaye zaman lafiya ta kasashen yankin tsakiyar Afrika ta FOMAC, a Jamhuriyar Afrika ta tsakiya na samun karin dakaru daga kasashe makwabta da suka hada da sojoji kusan dari da ashirin daga kasar Congo.

Kafin haka dai, Kwamandan rundunar ta FOMAC ya ce dakarun za su yi iya kokarinsu domin kare garin Damara daga dakarun 'yan tawayen da suka samu turawa gaba mai dama zuwa Bangui babban birnin kasar, da ragowar nisan kilomita 75.

Karin bayani