Rahotanni na cewa yawan mutanen da suka mutu a Syria sun kai dubu sittin

hare hare a Syria
Image caption hare hare a Syria

Majalisar Dinkin Duniya ta ce yanzu tana ganin mutanen da suka mutu a yakin basasar da ake yi a Syria ya kai dubu sittin.

Kwamishinar Kare Hakkin bil Adama ta Majalisar Dinkin, Navi Pillay, ta fada a birnin Geneva cewa yawan wadanda suka rasun ya zarce yadda suka zata a baya, kuma hakan yana da matukar tada hankali.

Yayin da hakan kuma ke faruwa, rahotannin baya-bayan daga Syriar sun ambaci 'yan tawaye na cewa wani hari ta sama da sojin gwamnati suka kai a kan wani gidan mai ya halaka mutane fiye da saba'in da biyar.

Shaidu sun ce sun ga konannun gawarwaki bayan harin a unguwar Mleiha, dake bayan birnin na Damascus.

An ce mata da yara na daga cikin wadanda suka mutu din.