An kashe kwamandan masu fafutika a Pakistan

nazir
Image caption Mullah Nazir

Rahotanni daga arewa maso yammacin Pakistan sun ce an kashe wani kwamandan masu fafutika, Mullah Nazir a wani hari da sojojin Amurka suka kai da wani jirgin yaki maras matuki.

Jami'an kasar ta Pakistan sun ce an harba makamai masu linzami daga jirgin kan motar Mullah Nazir a yankin kudancin Waziristan, kusa da iyaka da Afghanistan, kuma harin ya hallaka shi tare da wasu karin masu fafutika 5.

Wakilin BBC ya ce "Idan ta tabbata cewa an kashe Mullah Nazir, kamar yadda jami'ai a nan ke ikirari, to hakan zai kasance wata muhimmiyar nasara ga Amurka, wadda a baya ta yunkurin hallaka shi sau da dama".

Mullah Nazir dai ya taka muhimmiyar rawa wajen samar da mayakan da za su yaki sojojin kawance a Afghanistan.

Karin bayani