Sudan ta Kudu ta zargi Jamhuriyar Sudan

Omar Al Bashir da Silva Kiir
Image caption Ana shirin tattaunawa tsakanin Omar Al Bashir da Silva Kiir

Sudan ta Kudu ta zargi Jumhuriyar Sudan makwabciyar ta da kai ma ta hari, yayinda shugabannin kasashen biyu ke shirin gaanawa.

Wani kakakin rundunar sojin Sudan ta Kudu, Philip Aguer, ya ce sojojin gwamnatin Jumhuriyar Sudan sun kai hare-hare ta sama da kuma ta kasa a jihar Bhar-el-Ghazal a jiya Laraba.

A ranar Juma'a ne dai aka shirya shugaban Sudan ta Kudu, Silva Kiir zai gaana da takwaran aikinsa na Jumhuriyar Sudan Omar al Bashir a kasar Habasha.