'Yan adawa a Venezuela na son bayani kan lafiyar Chavez

Shugaba Hugo Chavez naVenezuela
Image caption Shugaba Hugo Chavez na Venezuela

Gamayyar jam'iyun adawa a Venezuela sun nemi cikakken bayani game da rashin lafiyar shugaba Hugo Chavez makonni uku bayan da aka yi masa tiyata a kasar Cuba.

Wannan bukata ta 'yan adawar dai na zuwa ne bayan da wasu jami'an kasar suka bayyana cewa Mr Chavez na cikin wani mawuyacin hali sakamakon matsalar daya samu a tiyatar da aka yi masa, sai dai sun jaddada cewa yana numfashi kuma yana samun sauki sannu a hankali.

Nan da mako guda ne dai ya kamata Mr Hugo Chavez, wanda aka sake zabensa a matsayin shugaban kasar a watan Oktoba ya sha rantsuwar kama aiki, sai dai gwamnatin kasar ta ce za'a jinkirta yin hakan kasancewar bashi da koshin lafiya.

Wannan mataki dai ya yi matukar harzuka bangaren 'yan adawa a kasar inda shugaban gamayyarar 'yan adawan Ramon Aveledo ya nanata cewa kamata yayi a gudanar da wani sabon zabe kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanadar maimakon ci gaba da rufa rufa game da rashin lafiyar shugaban kasar.