Bajekolin fasahar kere-kere a Amurka

LED
Image caption Sabuwar talabijin din ita ce mafi girma a yanzu

Kamfanin lataroni na LG ya fara karbar odar akwatunan talabijin samfurin LED, wanda shi ne mafi girma yanzu a kasuwa a kan kudi dala dubu goma.

Talabijin din mai siririyar fuska na nuna hoto rangadadau, kawo yanzu ana samusa ne kawai a manyan wayoyin tafi da gidanka da kwamfyutar hannu.

A mako mai zuwa shirin fasaha na BBC click, zai kashe kwarkwatar ido, a bajekolin fasahar kere-kere ta duniya da za a yi a Las Vegas na Amurka, inda za ku ji wasu labaran game da talabijin samfurin na LED.

Rage gurbatacciyar iska a China

Kudurin China na sabuwar shekara zai zamo na rage gurbatacciyar Iskar Carbon ne, da kuma zuba jarin dalar Amurka biliyan 56 don tsaftace yanayi a kasar.

China ta kuma fara sabunta bayanai game da matakin gurbacciyar iskar a manyan biranenta 74.

Rahoton kungiyar kare muhalli ta greenpeace ta ce gurbatacciyar iska a China ta rubanya abin da hukumar lafiya ta duniya ta iyakance.

Karin bayani