Ana bikin zagayowar kafa kungiyar Fatah

Shagulgula a Gaza
Image caption Shekaru arba'in da takwas da kafa Fatah.

A ci gaba da sasanta alaka tsakanin jam'iyyun Palasdinu masu adawa da juna, Fatah da Hamas, a yanzu haka ana gudanar da wani gagarumin gangami a zirin Gaza domin bikin cikar shekaru arba'in da takwas da kafa Fatah.

Hamas, wacce ita ke mulkin zirin Gaza, ta ba da izinin yin taron ne a karo na farko tun bayan da ta karbi mulki a shekarar dubu biyu da bakwai.

A watan jiya ne magoya bayan Hamas su ka yi na su bikin murnar kafuwar da wani gangami da ba'a saba irinsa ba a gabar yammacin kogin Jordan da ke karkashin ikon Fatah.

Karin bayani