Majalisar dokokin Amurka ta amince da tallafin kudin guguwar Sandy

Shugaban Amurka Barrack Obama
Image caption Shugaban Amurka Barrack Obama

Majalisar dokokin Amurka ta amince da kimanin dala biliyan goma a matsayin kudin tallafi ga wadanda bala'in guguwar Sandy ta rutsa dasu a watan Oktoban shekarar data gabata.

Rashin amincewa da wannan kudiri da Majalisar bata yi ba a farkon wannan makon dai ya haddasa kakkausar suka daga 'yan siyasa na Jam'iyun Republican da Democrat wadanda suka fito daga jihohin da bala'in yafi muni.

An dai shirya wannan kudiri ne ta yadda zai iya biyan kudaden inshora da yawansa ya kai dubu dari da ashirin a wani yunkuri na bada tallafi ga wadanda bala'in ya rutsa dasu da aka kiyasta cewa zai kai kimanin dala biliyan sittin, wanda kuma tuni Majalisar dattawan kasar ta amince da shi baki daya a makon jiya.

Kuma kamata ya yi Majalisar wakilan ta amince da kudirin dokar ba tare da wata matsala ba, sai dai bayan da aka dauki wani lokaci ana tattaunawa don kaucewa watsi da kudirin, Kakakin Majalisar John Boehner ya ki gabatar da batun gaban Majalisar domin a kada kuri'a, inda wasu mukarrabansa suka bayyana cewa kasancewar kudirin ya kunshi wani gagarumin shiri ne na kashe makuden kudade, to kuwa kamata yayi a jira sai lokaci yayi.

To sai dai kuma a wani yunkuri na nuna hadin kai tsakanin 'yan Majalisu, an yi ta tada jijiyar wuya tsakanin 'yan siyasa da suka fito daga jihohi biyu da bala'in guguwar tafi kamari, wato jihohin New Jersey da New York.

A cewar gwamnan jihar New Jersey, jinkirin wani babban abun kunya ne.

Sai dai Mr Boehner, wanda yayi ta shan suka daga 'yan jam'iyarsa ta Republican ya fahimci cewa ba zai iya ci gaba da jan kafa ba game da batun, inda ya bayyana cewa za'a kada kuri'ar neman amincewa da kudirin da ya kunshi sauran dala biliyan hamsin a ranar sha biyar ga wannan watan.

To sai dai kasancewar kudirin ya kunshi wasu aikace-aikace ne da basu da alaka da bala'in guguwar ta Sandy, mai yiwuwa a dauki wani dogon lokaci kafin a amince da sauran bukatun dake kunshe a cikin kudirin.