An cafke masu haramtaccen cinikin kodar bil adama a India

'Yan sanda a India
Image caption Zargin gudanar da haramtaccen cinikin koda a India

'Yan sanda a kudancin Indiya sun ce sun cafke mutane bakwai bisa zargin haramtaccen cinikin kodar bil adama.

Ana tuhumar mutanen, da suka hada da ma'aikatan gwamnati ne da cirar kodar talakawa ta hanyar tiyata domin yiwa masu kudi dashe.

Masu shigar da kara sun yi zargin cewa mutanen na bincinawa talakawan dan abinda bai taka kara ya karya ba daga cikin dimbin kudin da suke cazar masu sayen kodar.

Cinikin sassan jikin mutum dai haramun ne a dokar Indiya sai dai ana fargabar cewar ba'a aiwatar da dokar yadda ya kamata.

Karin bayani