An shiga rudanin Shugabanci a Venezuela

Hugo Chavez
Image caption Shugaba Chavez ba shi da koshin lafiya

Majalisar dokokin Venezuela na zama na musamman a yau, yayinda ake cigaba da rudani game da ikon shugaba Hugo Chavez na fara wani sabon wa'adin mulki.

Ana dai sa ran majalisar za ta zabi wani na hannun daman Mr. Chavez, Diyosdatho Kabellyo ne a matsayin shugaba.

Wakiliyar BBC a Caracas, babban birnin Venezuela ta ce Mr Kabellyo zai iya zama shugaban rikon kwarya idan Mr. Chavez mai shekaru hamsin da takwas ya gaza.

Shugaba Chavez dai na farfadowa ne daga tiyatar da aka yi masa a Cuba saboda cutar Cancer, wato daji, kuma ana jin bai yi kwarin da zai iya halartar bikin rantsar da shi a ranar Alhamis mai zuwa ba.

Karin bayani