Karin kudin mai ya janyo rikici a Bangladesh

  • 6 Janairu 2013
Bangladesh
Image caption An kwafsa tsakanin 'yan sanda da jama'a a Bangaladesh

'Yan sanda a Bangladesh sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye da kuma harsasan roba, domin tarwatsa dandazon 'yan adawa dake zanga-zanga a Dhaka, babban birnin kasar.

Babbar jam'iyyar adawa ta BNP ce ta shirya gangamin yini guda a fadin kasar domin nuna rashin amincewa da karin farashin albarkatun man fetur da aka yi a kwanan nan.

Makarantu da ofisoshi da dama dai sun rufe a yau, yayinda mahukunta suka baza 'yan sanda a kan tituna.

Wannan ne dai karo na biyar da gwamnatin ta kara farashin fetur, da diesel, da kananzir, inda tace wajibi ta janye tallafin da ta ke bayarwa.

Karin bayani