Amurka ta yi fatali da tayin Assad

Image caption Shugaba Barack Obama na Amurka

Amurka ta yi fatali da tayin da Shugaba Assad ya yi na tabbatar da zaman lafiya a Syria, tana cewa yunkuri ne kawai na makalewa a kan kujerar mulki.

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Amurka, Victoria Nuland, ta ce gwamnatin Shugaba Assad ta sarayar da halalcinta don haka ya kamata ta san na yi.

Da ya ke jawabi ga dimbin magoya bayansa a Damscus, Shugaba Assad ya ce ba su taba juya baya ga masalaha ta siyasa ba.

Amma fa Shugaba Assad ya kara da cewa ba za su hau teburin shawarwari da mutanen da ba abin da suka yi amanna da shi sai zub da jini da ta'addanci ba.

Kasashen Turkiyya, da Burtaniya, da ma Tarayyar Turai sun yi suka a kan jawabin suna jaddada kira ga Shugaba Assad ya yi murabus.

Karin bayani