Za a kayyade kadarorin Bankuna

Image caption Kudaden Euro

A karon farko, manyan bankunan kasashe da hukumomi masu sa ido kan hada-hadar kudade, sun amince da wasu ka'idoji da ke kayyade adadin kudi tsaba ko kadarorin da bankuna za su mallaka, a wani yunkuri na gujewa sake afkawa cikin matsalar tattalin arziki a duniya.

Kwamitin sa ido kan harkar banki na Basel dake Switzerland ne ya yanke shawarar da nufin tabbatar da cewa, ko wanne banki zai iya tsayawa da kafafunsa har tsawon wata guda ba tare da tallafin gwamnati ba idan ya fada mawuyacin hali.

Sai dai kwamitin ya baiwa bankunan wa'adin zuwa shekarar 2019 su kammala cika sharuddan da aka gindaya; an samu karin shekaru hudu ke nan a kan wa'adin da aka zata tun farko.

Sai dai bankunan sun yi korafin cewa idan ka'idoji suka fiya tsauri za su takure kofofin ba da rance.

Karin bayani