An rantsar da shugaba Mahama na Ghana

Image caption Dubban jama'a ne suka taru a dandalin Black Stars domin bikin rantsuwar

An rantsar da shugaba John Mahama na kasar Ghana a wani biki a birnin Accra bayan da ya lashe zaben shugaban kasar a watan Disambar da ya gabata.

Sai dai babbar jam'iyyar adawa ta NPP ta kauracewa bikin tana mai zargin cewa an tafka magudi a zaben da ya bashi nasara.

Mr Mahama ya samu kashi 50.7% cikin dari abin da ya bashi nasara kan dan takarar jam'iyyar NPP Nana Akufo-Addo, wanda ya samu kashi 47.7%.

Kungiyoyin masu sa ido na kasashen waje sun ce an gudanar da zaben cikin inganci da kuma adalci.

John Mahama ya kasance shugaban kasar ta Ghana ne tun lokacin da tsohon shugaban kasar John Atta Mills ya rasu a watan Yulin shekara ta 2012.

Karin bayani