Kudaden shigar Iran sun ragu

Wata tashar jiragen ruwan Iran
Image caption Wata tashar jiragen ruwan Iran

Shugaban kwamitin kasafin kudi na Majalisar dokokin Iran, ya ce yawan kudaden shigar da ƙasar ke samu daga man fetur da iskar gaz, ya ragu da kashi 45 daga cikin 100 a cikin watanni 9 da suka wuce.

Furucin na Gholam Reza Kateb dai, wata alama ce ta amsa cewa takunkumin da ƙasashen duniya suka saka wa Iran din, bisa shirinta na nukiliya, yana yin matuƙar illa ga tattalin arzikin ƙasar .

Amurka da ƙawayenta dai sun yi imanin cewa Iran na kokarin ƙera makaman nukiliya ne.

A cikin 'yan watannin da suka wuce ma, darajar kudin Iran din ta fadi warwas, abun da ya janyo kakkausar suka a kan gwamnatin ƙasar, bisa gazawar da ta yi wajen farfado da tattalin arzikin ƙasar.