'Yan bindiga sun kashe wasu mutane a Kano

Wasu 'yan sandan Najeriya
Image caption Tsaro ya tabarbare a Arewacin Najeriya a 'yan shekarun nan

Rahotanni daga jihar Kano a arewacin Najeriya na cewa wasu 'yan bindiga sun bude wuta kan wasu mutane inda suka kashe kimanin mutane uku.

Lamarin ya faru ne a kusa da gidan Zoo da ke birnin Litinin da yamma bayan Sallar Magariba.

Wasu da ke yankin sun ce 'yan bindigar sun je wajen ne a kan babura inda nan take suka bude wuta kan jama'ar da ke wurin, kafin daga baya su tsere.

Rundunar tsaron hadin gwiwa da ta 'yan sandan jihar ta Kano sun tabbatar da lamarin, sai dai sun ce suna kokarin tattara bayanai.

A baya ma dai an sha kai irin waÉ—annan hare- hare a yankin na gidan Zoo inda a kwannan nan ma aka kashe wasu mutane biyu a wani shagon saida kaya.

Karin bayani