An kori wasu 'likitoci' a Nijar

Shugaba Issoufou Mahamadou
Image caption Shugaba Issoufou Mahamadou ya lashi takobin yaki da zamba a Nijar

A jamhuriyar Nijar hukumomin kiwon lafiya na ƙasar sun kori wasu likitoci talatin da uku daga aiki.

Hukumomin sun samu uku daga cikinsu ne da laifin amfani da takardun shaidar kammala karatu na boge.

Hakan dai ya biyo bayan wani bincike ne da gwamnatin Nijar ɗin ta aiwatar tare da hadin gwiwar ƙungiyar ƙwararrun likitoci ta ƙasar, Synphamed.

Amfani da takardun shaidar kammala karatu na boge ya fara zama ruwan dare a ƙasar ta Nijar inda ko a kwanakin baya hukumar 'yan sanda ta ƙasa ta kori wasu ɗaliban 'yan sanda daga makarantar koyon aikin 'yan sandan, bisa amfani da takardun shaidar karatu na bogi.