Obama ya mika sunan Hagel don zama Sakataren tsaro

Shugaba Obama da Senata Hagel da kuma John Brennan
Image caption Shugaba Obama da Senata Hagel da kuma John Brennan

Shugaba Obama ya gabatar da sunan Senata Chuck Hagel na jam'iyyar Republican domin zama sabon Sakataren tsaron ƙasar.

Mr Obama ya bayyana cewa Mr Hagel zai kafa tarihi idan ya rike wannan muƙami.

Ya ce Mr Hagel zai kasance mutum na farko a wannan muƙami da ya yi aikin soja, kuma daya daga cikin jami'ai 'yan tsiraru a wannan muƙami da suka samu raunika a lokacin yaƙi, sannan kuma tsohon soja na farko da ya taɓa samun lambar girma bayan yaƙin Vietnam.

Kodayeke da ma an sa ran cewa Mr Hagel din ne zai samu muƙamin, amma wasu 'ya'yan jam'iyyarsa ta Republican sun soki lamirinsa, suna ma su cewa yana yiwa Iran sassauci, kuma yana ƙyamar Isra'ila.

Masu aiko da rahotanni sun ce Mr Obama zai fuskanci ƙalubale a majalisar dokokin Amirka kafin ya iya samun biyan buƙata.

Hakazalika shugaba Obama ya zabi John Brennan mai ba shi shawara kan yaki da ta'addanci domin ya zama sabon shugaban kungiyar leken asiri ta CIA.