Congo: 'Yan tawayen M23 sun tsagaita wuta

Mayakan M23
Image caption 'Yan tawayen sun karbe garin Goma a watan Nuwambar bara, amma daga bisani suka janye

'Yan tawayen M23 sun tsagaita wuta don kashin kansu, gabannin zagaye na biyu na tattaunawar zaman lafiya da gwamnatin demokradiyyar Congo.

Sun bayyana hakan ne a wani taron manema labarai a Kampala, suna masu fatan cewa ita ma gwamnati da ta bi sahunsu.

Yunkurin tattaunawar da aka yi a watan jiya na kawo karshen tada kayar bayan na tsawon watanni tara bai yi nasara ba.

Kimanin mutane 800,000 ne suka rasa matsugunansu, tun lokacin da 'yan tawayen suka fara yaki da gwamnati a watan Mayun shekarar 2012.

"Muna goyon bayan zaman lafiya, kuma a yau mun sanar da tsagaita wuta." Kamfanin dillacin labarai na Reuters ya ambato kakakin kungiyar ta M23, Francios Rucogoza na cewa a Kampala.

"Koda kuwa gwamnati ta ki amince wa ta tsagaita wuta, mun amince za mu cigaba da tattaunawa." Inji Kakakin.

'Yan tawayen dai na zargin shugaba Joseph Kabila da rashin aiwatar da yarjejeniyar baya, wadda a karkashinta za a shigar da su cikin sojin kasar.

Tun asali, mutumin da kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ke nema ruwa a jallo, Bosco Ntaganda ne ke jagorantar kungiyar M23, kuma sun samu nasarori a bara.