Mutane miliyon daya na fama da yunwa a Syria

syria
Image caption Kananan yara na fama da yunwa a Syria

Majalisar dinkin duniya tace al'ummar Syria kusan miliyan daya na fama da yunwa yanzu haka, kuma dalili shine saboda yadda gwamnati ta takaita aikin rarraba tallafin abinci.

Hukumar samar da abinci ta majalisar dinkin duniya ta ce tana taimakawa mutane miliyan daya da rabi a Syria a kowanne wata, amma bai kai wanda ake bukata ba.

Hukumar samar da abincin ta ce ba zata iya kara tallafin da take bayarwa ba, saboda cibiyoyin da aka baiwa izinin irin wannan aiki a Syrian basu da yawa.

A wata alama ta karuwar matsalar ayyukan agajin, majalisar dinkin duniyar ta ce 'yan gudun hijira kusan dubu dari ne suka tserewa rikicin kasar a watan daya gabata.

Karin bayani