Garkuwa da mutane na karuwa a Maiduguri

Malam Abubakar Shekau
Image caption Malam Abubakar Shekau

A Najeriya, yanzu haka mazauna birnin Maiduguri babban birnin jihar Borno, dake arewacin kasar sun sake fadawa cikin halin zullumi, bayan wasu jerin sace-sacen jama'a a cikin makon nan.

A kwanaki biyun da suka gabata ne dai wasu 'yan bindiga suka sace wani babban dan kasuwa, Alhaji Ali Budum, a kan hanyarsa ta komawa gida daga shagonsa.

Bayanai sun ce 'yan bindigar sun sako dan kasuwar ne sa'oi da dama bayan sun karbi wasu makudan kudaden fansa.

Hakan kuwa na faruwa ne sa'o'i kadan bayan sace wata budurwa da wasu 'yan bindigar suka yi, wacce daga bisani aka tsinci gawarta a wajen gari.

Lamarin da ke faruwa a Maidugurin, ya sa wasu sun fara zargin anya kungiyar Jama'atu Ahlil sunna Lidda'ati da aka fi sani da Boko Haram ke aikata hakan, ko kuwa wasu ne ke fakewa da sunansu?

Karin bayani