Ba zan sauka daga mulki ba — Bozize

Image caption Shugaba Francois Bozize

Yayin da wakilai daga bangarorin da ke rikici a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya ke taruwa don tattaunawa a Gabon, shugaban kasar Francois Bozize ya ce ba zai amince da bukatar 'yan tawaye cewa ya sauka daga kujerar shugabanci ba.

Mista Bozize ya ce ba zai tattauna a kan matsayinsa ba da mutanen da ya kira sojojin haya 'yan ta'adda.

Kawancen 'yan tawaye na Seleka dai ya kwace iko da manyan garuruwa da birane a makonnin da suka gabata, kuma yana barazanar kwace babban birnin kasar Bangui idan har Mista Bozize bai sauka daga mulki ba.

Wakilin BBC a birnin ya ce mutane na cikin fargaba, kuma su na ta tara kayan abinci.

Karin bayani