Kotun Venezuela ta amince da jinkirta rantsar da Chavez

chavez
Image caption Shugaba Hugo Chavez na jinya a Cuba

Babbar kotun Venezuela ta goyi bayan wata shawara da majalisar dokokin kasar ta yanke, ta jinkirta rantsar da Shugaba Hugo Chavez a wani wa'adin mulkin.

Shugabar kotun kolin kasar, Luisa Morales ta ce ba lallai bane sai an sake rantsar da shi, saboda sake zabar sa aka yi a matsayin Shugabankasa.

Mista Chavez yana asibiti yanzu haka a Cuba, bayan wani aikin tiyata da aka yi masa a kan cutar daji, kuma yayi fama da cutar huhu daga baya.

An jinkirta bikin rantsar da shi da aka tsara a ranar Alhamis.

Wakiliyar BBC ta ce "abinda 'yan adawa ke cewa shine kundin tsarin mulki ya sanya ranar goma ga watan Janairu a matsayin ranar da sabon wa'adin mulkin shugaban zai soma, saboda haka tunda baya nan, sai a nada shugaban rikon kwarya a Kasar".

Karin bayani