Sudan na kara shiga bala'i

Image caption Rikicin Sudan da 'yan tawaye na cusgunawa mutane

Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa bala'in da ake fama da shi a kudancin sudan, inda dakarun gwamnati ke yakar 'yan tawaye a kudancin Kordofan da lardin Blue Nile, zai kara kazancewa.

Majalisar Dinkin Duniyar ta ce mutane da dama na mutuwa yayin da wasu dubun dubata ke rayuwa ta hanyar cin ganyayyaki da jijiyoyin bishiya.

Wani babban jami'i mai kula da ayyukan jin kai na Majalisar, John Ging, ya dora laifi a kan gwamnatin Sudan da kungiyoyin 'yan tawaye.

Ya kuma bukaci taimakon Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya.

Acewar John Ging daya daga cikin matsalolin kungiyoyin bada agajin shi ne ba su da damar da za su taimakawa wadanda ke yankin da ake rikicin.

Karin bayani