A Najeriya an soki shirin bawa manoma wayar salula

Image caption Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan

Jam'iyyun adawa a Nigeria sun soki shirin gwamnati na rabawa manoma miliyan goma wayar salula kyauta.

An yi kiyasin cewa shirin zai lashe kusan dala miliyan dari hudu.

'Yan adawar sun ce akwai kanshin almundahana tattare da shirin, inda suka ce za a raba wayoyin ne ga magoya bayan gwamnati.

Gwamnatin dai ta ce manufar shirin ita ce bunkasa harkar noma a Nigeria, sannan rabin wayoyin za a raba su ne ga mata.

Karin bayani