Ba a cinye kaso 30 na abincin duniya— Rahoto

Image caption Abinci yayin da aka gama dafa shi

Wani sabon rahoto ya yi kiyasin cewa ba a cin kashi talatin zuwa hamsin cikin dari na abincin da ake nomawa a duniya.

Wata kungiyar injiniyoyi ta Birtaniya ta ce rashin ingantattun na'urorin girbi da na adana amfanin gona na lokaci mai tsawo da ma zurfafawa wajen kayyade lokacin sayo da kayan abincin na haifar da abin da ta kira kazamar barnar abinci.

Rahoton ya kuma ce ana zubar da rabin abincin da aka saya a kasashen Turai da Amurka.

Marubuta rahoton sun ce ana bukatar dabarun da suka dace don rage barnar abinci ganin cewa ana sa ran al'umar duniya za ta karu da mutum biliyan uku nan da karshen wannan karnin.