'Farautar namun daji na barazana ga Kenya'

Image caption Shugaban Kenya Raila Odinga

Firai ministan kasar Kenya ya yi kira ga kasashen duniya su taimaka a yaki abin da ya kira barazanar nan ta farautar giwaye.

Raila Odinga ya ce safarar namun daji babbar barazana ce ba kawai ga yunkurin kare muhalli ba har ma da doka da oda, kuma wajibi ne hukumomi a matakan kasa da duniya su kara zage dantse don maganin matsalar.

Ya kara da cewa masu farautar giwaye na kai mummunar bara a kan harkar yawon bude ido, wadda ke samar da kaso mafi tsoka na kudin shigar kasar.

A shekarar da ta gabata an kashe giwaye dari uku da sittin ba bisa ka'ida ba a kasar.