Sojin Mali na yunkurin kwace garin Douentza

Dakarun Mali
Image caption Dakarun gwamnati da masu fafutukar Islama sun yi artabu kusa da garin Konna

Dakarun sojin Mali sun yi wa garin Douentza kawanya, a wani yunkuri na karbe ikon garin dake hannun masu fafutukar Islama.

Kakakin sojin kasar, kanal Diaran Kone ne ya bayyana hakan.

Tun da fari, wata majiyar sojin ta ce dakarun gwamnati sun karbe garin, amma wani mazaunin garin ya musanta hakan.

Masu fafutukar Islama dai sun karbe iko da arewacin kasar, watanni tara da suka gabata, bayan sun fatattaki dakarun gwamnati.

A ranar Talatar da ta gabata ne, shugaban kungiyar Tarayyar Afrika, Thomas Boni Yayi ya bukaci NATO ta aika da dakaru Mali, domin yakar masu fafutukar Islama.

Wasu shugabanni a nahiyar Turai sun bayyana fargabar cewa , masu fafukar Islaman za su iya amfani da yankin Mali dake karkashin ikonsu, wanda girmansa ya kai girman kasar Faransa, wajen kai hari kan nahiyar Turai.

Sai dai majalisar Dinkin Duniya ta ce sai nan da watan Satumbar shekarar da muke ciki ne, za a kai dakaru Mali.