An ƙaddamar da kundin ɗa'ar aikin 'yan sanda a Najeriya

Wasu 'yan sandan Najeriya
Image caption Wasu 'Yan Najeriya na zargin 'yan sanda da rashin iya aiki

A Najeriya, rundunar 'yan sandan ƙasar ta ƙaddamar da wani sabon kundi na ɗa'ar aikin 'yan sanda.

Kundin dai ya kunshi wasu ɗabi'u ne da ake buƙatar 'yan sanda su runguma ta yadda aikinsu zai inganta, kana su samu karɓuwa a wajen al'umma.

Jami'an 'yan sanda a Najeriya dai na fama da zargin cin hanci da rashawa da rashin iya gudanar da aiki.

Abun da ba'a sani ba dai shi ne ko wannan kundin ɗa'a zai maido da martabar 'yan sanda ta tun tuni, lokacin da ake yi ma su kirari da ɗan sanda abokin kowa.

Karin bayani