An kashe mutane da dama a Pakistan

Fashewar bam a Quetta
Image caption Birnin Quetta ya sha fama da tashin bama-bamai

'Yan sanda a Pakistan sun ce an kashe aƙalla mutane tara bayan wasu tashin wasu bama- bamai biyu a jere a wajen wani wurin wasan Snooker a garin Quetta dake kudu maso yammacin ƙasar.

Tun da farko mutane goma sha ɗaya ne aka kashe a sakamakon fashewar wani abin daban a wani yanki dake da cunkoson jama'a, kuma wasu ƙarin mutane da dama sun jikkata.

Rahotanni sun ambato 'yan sanda suna cewa wata tukunyar iskar gas ce ta janyo fashewar abin a cikin wani dakin girki.

Garin na Quetta dai wanda shi ne babban birnin lardin Baluchistan, ya yi fama da aikace- aikacen masu tada ƙayar baya shekara da shekaru.

Karin bayani