Chavez zai ci gaba da mulki a Venezuela

Image caption Hugo Chavez na fama da rashin lafiya

Kotun kolin kasar Venezuela ta yanke hukuncin cewa Shugaba Hugo Chavez da gwamnatinsa ka iya ci gaba da mulki, duk da cewa shugaban kasar ba shi da cikakkiyar lafiyar da zai halarci bikin rantsar da shi.

Mista Chavez ya na asibiti a Cuba bayan aikin da aka yi masa na cutar sankara, kuma a cikin kimanin wata guda ba a gan shi a bainar jama'a ba.

Shugaban 'yan adawa Henrique Caprile ya amince da hukuncin kotun kolin, amma ya ce hakan ba zai kawo karshen rashin tabbas a Venezuela ba.

Shugaban Majalisar dokokin Kasar Diosdado Capello ya yi kira ga magoya bayan shugaban su fito kwansu da kwarkwatarsu don nuna goyon baya ga shugaban.

'Yan adawa kuwa kiran magoya bayan su suka yi da su kauracewa kan tituna don gujea arangama da masu marawa Shugaban Kasar baya.

Karin bayani