Lamura sun fara gyaruwa a Damaturu

Wani hari kan ofishin yansanda a Damaturu
Image caption Wani hari kan ofishin yansanda a Damaturu

Jama'a na ci gaba da komawa gidajensu tare da sana'o'insu a garin Damaturu, babban birnin jihar Yobe.

Hakan ya biyo bayan kauracewa garin na tsawon watanni da suka yi sakamakon matsalar tsaron da aka sha fama da ita a garin.

Matsalar da ake dangantawa da tashe tashen hankulan da kungiyar nan ta Boko Haram ke haddasawa.

Mutanen da wakilinmu ya tattauna da su sun ce yanzu kam sai hamdala domin kuwa lamura sun fara komawa yadda suke a baya a garin.