Za a kafa gwamnatin hadaka a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya

'Yan tawaye a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya
Image caption Za a kafa gwamnatin hadaka

Gwamnatin Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya da kungiyoyin 'yan tawaye sun amince da kafa gwamnatin hadaka, a wani bangare na yarjejeniyar da suka rattaba hannu a tattaunawar sulhu.

Bangarorin biyu dai sun fara tattaunawa ne a ranar Laraba a Libreville, babban birnin Gabon.

Sun kuma amince da gudanar da zabe cikin shekara guda tare da nada firaminista daga bangaren 'yan adawa.

A watan jiya ne 'yan tawayen suka koma bakin daga a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiyar tare da kame wasu garuruwa, har suka isa daf da Bangui babban birnin kasar.

Karin bayani