Dakarun Faransa sun isa Mali

 Francois Hollande na Faransa
Image caption Za a fafata da dakarun Faransa a Mali

An tura dakarun Faransa kasar Mali domin fafatawa da 'yan tawaye.

Shugaban kasar Faransa, Francois Hollande, ya ce za su cigaba da dauki-ba-dadi da 'yan tawayen har sai sun yi nasara a kansu.

Wani hafsan soji a Mali yace dakarun Faransar sun fari kai harin ne tare da sojojin Senegal da Najeriya.

Gwamnatin Mali dai ta nemi taimakon Faransa wacce ita ta yi ma ta mulkin mallaka ne bayanda 'yan tawayen da ake dangantawa da kungiyar al-Qaeda su ka kwace garin Konna.

Tarayyar Turai tace lamarin na bukatar daukin gaggawa da kasashen duniya yayinda Faransa ta shawarci 'yan kasarta da su fice daga Mali.

Karin bayani