'Yan sanda sun fitar da rahoto kan Jimmy Savile

Jimmy Savile
Image caption An zargi Jimmy Savile da cin zarafin kananan yara

Wani rahoton 'yan sanda game da tsohon fitaccen mai gabatar da shirye-shiryen talabijin na BBC, Jimmy Savile, yace marigayin ya kwahe shekaru sittin ya na lalata da kananan yara.

Rahoton ya yi bayani kan kananan yara fiye da dari wadanda shekarunsu suka gaza sha takwas ciki ma har da dan shekara takwas da Jimmy Savile din ya yi lalata da su.

Rahoton yace da an saurari korafe-korafen yaran tun da fari da an kai ga hukunta shi kafin mutuwarsa.

Jimmy Savile dai ya aikata lalatar ne a cikin harabar BBC da kuma asibitocin da ya yi aikin sa kai.

Kafin dai rasuwarsa a bara, Jimmy Savile ya samu lambar girma daga Sarauniya Elizabeth ta biyu saboda aiyukan da ya yi na tallafawa mabukata.

Abin kunyar da ya biyo bayan fallasar tabargazar da ya yi dai ya haddasa ajiye aikin Darakta Janar na BBC George Entwistle.