A shirye Faransa take ta taimakawa Mali

Mayaka masu kishin Islama a Mali
Image caption Mayaka masu kishin Islama a Mali sun kame garin Konna.

Shugaba Fancois Holande na Faransa ya ce a shirye Faransa take ta dakatar da dannawar da 'yan tawaye masu kaifin kishin Islama suke a Mali.

Ya ce, Faransa za ta yi aiki ne bisa izinin majalisar dinkin duniya, wadda ta bukaci gaggauta tura dakarun kasa da kasa a wani taron gaggawa na kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya.

Shugaban Francois Hollande ya yi tattaunawar gaggawa da ministan tsaro da kuma na harkokin wajen a kan yadda lamura ke kara rincabewa a kasar Mali, musamman wasikar da shugaban Mali Traore ya aike don neman taimakon sojin Faransa.

Kamar yadda jami'an Faransa suka bayyana, majalisar dinkin duniya tuni ta amince da batun kaiwa Mali agaji.

Kodayake dai ba a bayyana irin agajin da za a kaiwa kasar ba, saboda haka akwai yiwuwar yin luguden wuta ta sama don hana 'yan tawaye nausawa zuwa cikin garin Mopti.

A ranar Laraba ne ake sa ran Shugaba Traore na Mali zai ziyarci Faransa don ganawa da shugaba Hollande don tattauna irin yadda Faransar zata kawo dauki cikin hanzari.