Mutane sama da dari aka kashe a Pakistan

Harin bom a birnin Quetta, kasar Pakistan
Image caption Harin bom a birnin Quetta, kasar Pakistan

Sama da mutane dari ne aka kashe, wasu da dama kuma suka jikkata a jerin hare-haren bama bamai a Pakistan.

Mafi munin asarar rayukan ta faru ne a tagwayen harin da aka kai a wani wajen wasan kwallon tebur na Snooker , a birnin Quetta da ke kudu maso yammacin kasar.

Ma'aikatan agaji da 'yan jarida da dama ne suka rasa rayukansu a tashin bam na biyu da ya ruguza ginin lokacin da suka garzaya wurin bayan tashin bam na farko.

Jami'an 'yan sandan sun ce fashewar ta abku ne a wurin da ke da tarin jama'a, kusa da wata mota mai dauke da wasu jami'ai masu kayan sarki,kuma galibin wadanda suka mutun musulmai ne 'yan shia.

Birnin Quetta dai ya shafe shekaru da dama yana fama da tashe-tashen hankula da suka hada da kaddamar da hare-hare, a yankunan aka girke jami'an tsaro na Constabulary.

Wani harin bam din na daban da aka kai a kasuwar birnin na Quetta, ya hallaka mutane bakwai, kazalika can kuma a wani harin bam din sama da mutane 20 ne suka mutu a wajen wani taron addini a Swat.

Wata kungiyar musulmi mai fafutuka da makamai ta ce dai tayi ikirarin kai harin.