Ana zaman dar-dar a wasu sassan jihar Zamfara

Hare-hare a jihar Zamfara
Image caption Hare-hare a jihar Zamfara

Ana zaman dar-dar a wasu kauyukka uku a jahar zamfara, bayan wasu hare-haren wasu kungiyoyin 'yan fashi da makami suka kai musu.

Hare-haren dai sun yi sanadiyyar hasarar dimbin rayukka a karshen makon jiya.

Fiye da mutane 150 ne da suka rasa rayukkansu a cikin ire-ren wadannan hare-haren a kauyukka daban-daban na jahar, tun bayan somawar su a tsakiyar shekara ta 2011.

Hukumomi dai sun yi imanin cewar hare-haren na ramuwar gayya ne ga yadda kungiyoyin 'yan banga a kauyukkan ke fatattakar wadanda suke tuhumar 'yan fashi tare da karkashe su.