Faransa ta shiga wani hali

Shugaban kasar Faransa, Francois Hollande
Image caption Shugaban kasar Faransa, Francois Hollande

Shugaban kasar Faransa, Francois Hollande, yace zai kara tsananta tsaro a cikin kasar, saboda fargabar hare-haren daukar fansa game da tura dakarun Faransa Mali da Somalia.

Dakarun Faransa dai sun cigaba da lugudan wuta ta sama kan 'yan tawayen kasar Mali, sun kuma tura sojojin kasa su tsare Bamako, babban birnin kasar.

Ministan tsaron Faransa, ya ce an kashe a wani matukin jirgin yakin Faransa a karawar da aka yi ranar Juma'a.

Tunda fari dai dakarun Mali sun ce sun kwato garin Konna tare da tallafin dakarun Faransa daga hannun 'yan tawaye.

Karin bayani