Faransa ta gaza ceto sojanta

Mayakan Al-Shabab
Image caption Mayakan Al-Shabab

An kashe sojan Faransa daya yayinda guda kuma ya bace a yunkurin da suka yi na kwato wani bafaranshe da aka yi garkuwa da shi a Somalia.

Ministan tsaron Faransa yace dakarun na musamman ba su yi nasarar kwato mutumin da aka yi garkuwar da shi ba, inda suka gamu da tsatstsaurar tirjiya.

Kungiyar Al-Shabab dai ta ce mutumin da su ka yi garkuwar da shi na nan da ransa kuma su ne su ka cafke wanda ake cewa ya bace.

Mazauna garin Bulo Marer dake kudancin Somalia, sun kwatanta cewa dakarun kasashen wajen sun dira da jirginsu mai saukar angulu akan kwanon wani gida da 'yan gwagwarmaya ke amfani da shi. Sun ce an kashe akalla fararan hula hudu da suka hada da wata mata mai juna biyu a musayar wutar da akai.