Kotu a Najeriya ta yi watsi ta wani matakin hukumar zaben kasar

Taswirar Najeriya
Image caption Taswirar Najeriya

Wata kotu a Najeriya ta yi watsi da matakin hukumar zaben kasar na soke takardar shaidar lashe zaben Majalisar dokoki a jihar Katsina da ta yi wa wasu 'yan Jam'iyar CPC.

A hukuncin da ta zartar, kotun ta ce matakin da hukumar zaben kasar ta dauka na soke takardar lashe zaben Majalisar dokoki , tare da mika sabbbin takardun ga wasu 'yan Jam'iyar ta CPC da hukumar zaben a watan Disambar shekarar 2011 ya saba ma doka.

A lokacin da take yanke hukunci, Mai shari'a Gladys Olotu ta bayyana cewa a bisa hujjojin da masu shigar da kara suka gabatar, kotun ta gamsu cewar sune zababbu 'yan majalisun dokoki daga jam'iyar CPC a jihar Kastina, a zaben shekara ta 2011.

To sai dai kuma Uwar jam'iyyar ta CPC ta ce za ta daukaka kara kan wannan hukunci.