Sojojin Faransa sun fara aiki a kasar Mali

Mayaka a kasar Mali
Image caption Mayaka a kasar Mali

Sojojin Faransa sun shiga kai farmaki kan 'yan tawaye 'yan kishin Islama a kasar Mali, da suka karbe garin Konna cikin makon nan.

Ministan harkokin wajen Faransa Laurent Fabius, ya bayar da tabbacin haka, yana cewar farmakin ya hada har da hari ta sama.

Shugaba Francois Hollande, ya bayyana 'yan tawayen wadanda ke da alaka da kungiyar Al-qaeda, a matsayin 'yan ta'adda wadanda ke barazana ga dorewar kasar ta Mali a matsayin kasa.

Sojojin kasar Malin sun ce da taimakon sojojin kasashen waje a yanzu an sake kwato Konna garin nan mai muhimmanci dake tsakiyar kasar.

Kasar Faransar ce ta aike da sojojin nata zuwa kasar ta Mali, kamar yadda gwamnatin kasar ta nema, don taimaka mata wajen yakar 'yan tawaye masu kaifin kishin Islama da suka riga suka karbe sama da rabin kasar.

Shugaban kasar Faransa Francois Hollande, ya ce ya karbi neman bukatun aikewa da sojojin ne saboda abinda ya ce 'yan ta'adda na neman daidaita kasar ta Mali.

An kuma bayar da rahoton aikewa da sojojin kasashen Senegal da Najeriya.

A wani jawabi da aka watsa a kafar yada labarai, shugaban kasar Mali Dioconda Traore yayi alkawarin murkushe yunkurin mayakan 'yan tawayen.

A cikin makon nan ne dai 'yan tawaye masu kaifin kishin Islamar suka kwace karfin iko a garin Konna, kana sun tilasta aiki da shari'ar musulunci a yankin arewacin kasar ta Mali.