Faransa ta tura sojojinta Somalia

Wasu sojojin Faransa
Image caption Wasu sojojin Faransa

Faransa ta tura sojojinta Somalia, a wani yunkuri da ya gaza samun nasarar ceto wasu mutanen da mayakan kungiyar Al-shabab suka yi garkuwa da su.

Bayanai sun ce wani sojan Faransa guda ya mutu a harin da suka kai, a yayinda wani Sojan ya bace.

Jami'an Faransa sun ce suna kyautata zaton mutumin da aka yi garkuwa da shi, wani jami'in leken asiri shima an kashe shi tare da 'yan kishin Islamar goma sha-bakwai da suka cafke shi.

Kungiyar Al-Shabab dai ta yi ikirarin cewa jami'in leken asirin da su ka yi garkuwar da shi na nan da ransa, kuma su ne su ka cafke wanda ake cewa ya bace.

Mazauna garin Bulo Marer dake kudancin Somalia, sun kwatanta cewa dakarun kasashen wajen sun dira da jirginsu mai saukar angulu akan kwanon wani gida da 'yan gwagwarmaya ke amfani da shi.

Sun ce a daren jiya sun ta jin karar bindigogi ana ta musayar wuta, kana jirage masu saukar angulu sun shiga fadan da ake gwabzawa, suna ta barin wuta ta sama, yayinda kana mayakan dake kasa na mayar da martani.

Sun kuma bayyana cewa babu wanda ke iya fita daga gidansa, amma da safe sun ga gawawwakin fararen hula uku.

Shugaban kasar Faransa Francois Holland dai ya ce Faransar ba za ta bada kai bori ya hau ba, wajen fafatawar da take da mayaka 'yan tawaye masu kaifin kishin Islamar.